Zazzaɓin Lassa Ya Kashe Ƙwararrun Likitoci Mata 2 A Nasarawa

Jaridar ‘The Guardian’ ta ruwaito cewa, likitocin sun gamu da ajalinsu ne bayan sun kamu da cutar a yayin wani aikin tiyatar gaugawa da suka yi wa wata mata mai ciki da ke zubar jini a asibitin kwararru na Dalhatu Arafat da ke Lafiya.

Wata majiya a asibitin ta tabbatar da cewa an kawo matar ne a gurguje a sabili da matsalar cutar lassa sabanin tunanin likitocin na cewa matsalar juna biyu ce.

Matar da jaririn da aka ciro daga cikinta dukkaninsu sun riga mu gidan gaskiya ‘yan awoyi bayan aikin tiyatar.

Majiyar asibitin ta kuma bayyana cewa, daya daga cikin likitocin da suka yi tiyatar ya rasu ne a makon da ya gabata inda sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa cutar lassa ce ta yi ajalinsa, shi ma abokin aikinsa ya mutu a cikin wannan makon.

Jami’ar hulda da jama’a ta asibitin, Ruth Naomi, ta tabbatar da cewa likitocin sun mutu ne a sakamakon cutar ta Lassa.

Idan za a iya tunawa dai a makon jiya ne ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce da yiwuwar barkewar zazzabin Lassa a jihar a yayin da aka samu rahoton samun mutane 2 dauke da cutar a jihar ta Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram