Yawan jami’an tsaron Najeriya da aka kashe a shekarar 2021 ya kai mutum 985.
Wani rahoto da kafar sadarwa ta BBC Hausa ta yi ya nuna cewa jami’an tsaron ƙasar da aka kashe sun kai mutum 985 a shekarar.
Rahoton ya ce daga cikin ɗari tara da tamanin da biyar da aka kashe mutum 642 sojoji ne, sai jami’an ƴan sanda su 322 da kuma jami’an Civil defence su 11.
Sauran jami’an sun haɗa da jami’an Kwastan 5 sai jami’an DSS da Immigration da kuma FRSC 5.
Duka kenan idan aka haɗa jumullarsu sun zama mutum 985.