Kotun Amurka Ta Daure Wani Magoyin Bayan Trump Kan Kutse A Majalisa

Kotun Amurka ta yanke wa wani mutum zaman gidan yari na tsawon shekaru 5 bayan kama shi da laifin jikkata ‘yan sanda yayin kutsen da magoya bayan Donald Trump suka yi a majalisar dokokin kasar.

Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa wannan ne hukunci mafi tsauri da aka yanke kawo yanzu ga mutanen da aka kama da laifin tayar da zaune tsaye a majalisar da ke birnin Washington.

Bayan yanke masa hukuncin, Robert Palmer ya fashe da kuka, inda ya ce ya ji kunyar laifin da ya aikata.

Rahoton ya bayyana cewa, Mista Palmer, a cikin wata wasika da ya rubuta wa alkali da hannunsa, ya ce, zancen tafka magudi karya ne, kuma Trump da magoya bayansa sun yaudare shi.

Kimanin mutane 700 ne dai aka kama da hannu a rikicin na Capitol.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram