Kungiyar Kwadago Ta Najeriya Na Shirin Yin Zanga-Zanga

Mai yiwuwa kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya, NLC, ta gudanar da zanga-zangar gama-gari a ranar 1 ga watan Fabrairun 2022.

Majalisar zartaswar kungiyar ce ta yanke shawarar daukar matakin da nufin nuna rashin amincewarta da yunkurin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.

BBC ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar ta NLC na kasa, Ayuba Wabba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar bayan taro da ya fitar a ranar Juma’a.

Kungiyar ta ce kafin gudanar da zanga-zangar ta kasa, za ta shirya wani maci a jihohin kasar 36 a ranar 27 ga watan Janairu duk da nufin matsa lamba ga gwamnatin shugaba Buhari kan ta dakatar da yunkurin na ta na cire tallafin tare da kara farashin man fetur a kasar.

NLC din ta ce cire tallafin zai jefa ma’aikata da sauran al’ummar kasar cikin karin kuncin rayuwa tare da haddasa tashin farashin kayayyaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram