Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya dake aiki da rundunar ‘yan sandan jihar Taraba sun kama wasu mutane 11 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Taraba.
An kama wadanda ake zargin ne saboda hadin kai da kuma rawar da suka taka a rikicin daya faru na sace-sacen jama’a a Taraba da suka hada da sace ma’aikatan Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, da yin garkuwa da wani dan uwan Sarkin Jalingo da kuma kashe wani Sajan na dan sanda a Jalingo Babban birnin jihar Taraba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunan Najeriya CP Frank Mba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi.
A cewarsa, “Rundunar ‘yan sandan ta kuma kwato bindigogi kirar AK47 guda bakwai, bindigogin Beretta guda biyu, alburusai masu rai daban-daban guda 121, da harsasai guda hudu, abun rufe fuska, haramtattun kwayoyi da sauran abubuwa masu tayar da hankali a yayin farmakin da suka kai maboyar wadanda ake zargin a jihar.
“Kamen wadanda ake zargin ya biyo bayan tura jami’an hukumar bayar da bayanan sirri da babban sufeton ‘yan sanda na kasa, IGP Usman Alkali Baba, ya yi zuwa jihar Taraba domin kara kaimi ga kokarin da rundunar ‘yan sandan jihar Taraba take yi tare da daukar matakai kan masu tayar da hankali na garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran munanan laifuka a jihar.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da suka hada da Luka Adam, Shuaibu Nuhu, Moses Amos, Peters Mashi, Ahmadu Mallam, Adamu Mohammed, Dahiru Mallam Dalha, Gambo Isah, Sanusi Ahmadu, Malam Mohammed Mauludu da Ibrahim Idi, dukkansu ‘yan asalin jihar Taraba ne.
Sannan yace, “Binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin suna cikin jerin sunayen da rundunar ‘yan sandan jihar Taraba suke nema ruwa a jallo, wadanda kuma ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane ne, kuma tabbas suna da alaka da yawaitar sace-sacen jama’a da akeyi a jihar da suka hada da kai harin da gangan kan jami’an tsaro .
Sannan Bincike ya kuma nuna yadda biyu daga cikin wadanda ake zargin, Gambo Isah da Sanusi Ahmadu suka shirya kisan wani Sajan na ‘yan sanda tare da raunata sufeto ‘yan sanda ta hanyar harbin bindiga a wani samamen da suka yi na baya-bayan nan don basu damar tserewa daga kama wasu da aka yi garkuwa dasu a Jalingo kwanan nan.
“Bincike ya kuma nuna cewa, modi operandi wadanda ake zargin sun hada da bin diddigin mutane – ’yan kasuwa, masu aikin gwamnati, masu ababen hawa dake dauke da manyan motoci, da dai sauransu zuwa gidajensu, daga nan kuma suka shirya da aiwatar da garkuwa da wadannan mutane, kuma suna tara makudan kudade a matsayin kudin fansa daga ‘yan uwa da abokan arziki kafin a sako su.
Sannan ‘Yan sanda a yayin gudanar da bincike sun gano tare da kai samame maboyar masu aikata laifuka daban-daban inda aka saba ajiye wadanda aka yi garkuwa dasu. A yayin da aka kwato tarin makamai da sauran abubuwan da ba a taba gani ba a maboyar tasu, duk wadanda aka yi garkuwa da su a maboyar sun yi tsanaki tare da samun nasarar kubutar da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma suka sake komawa zuwa ga iyalansu. A halin da ake ciki dai, masu bincike na ci gaba da kokarin kamo sauran wadanda ake zargin da aikata laifin.
Kazalika “IGP, yayin da yake yaba wa mutanen jihar Taraba nagari da suke baiwa ‘yan sanda goyon baya musamman wajen bayar da bayanai masu amfani da suka taimaka wajen kama wadanda ake zargin, ya kuma ba da tabbacin cewa ‘yan sandan za su ci gaba da hada kai da duk masu ruwa da tsaki wajen zurfafa tsaron hadin kan al’ummar Taraba. Sannan ya jajantawa iyalan marigayi Sajan Ogidi Habu, ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da kokarin inganta rayuwar al’umma a duk fadin Najeriya.
“Dukkan wadanda ake zargin za a gurfanar dasu Kotu, domin zartar masu da hukunci.