Ana zanga-zangar adawa da zaɓar Sarkin Etsu Nupe a Jahar Niger

Al’ummar garin Gaba da ke karamar hukumar Lavun a jihar Neja sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da zaben Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar a matsayin sabon sarkinsu.

Tsohon basaraken ya rasu ne a ranar 11 ga watan Oktoba shekarar 2021 kuma Etsu Nupe ya nada Alhaji Yusuf Gana a matsayin sabon sarkin al’ummar.

Shugaban kungiyar ci gaban Gaba, Mista Paul Y. Gana, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi zargin cewa fitaccen dan takarar da al’ummar yankin suka zaba domin cike gurbin kujerar, ba shi bane Wanda fadar Etsu Nupe ta nada.

Ya ce, “A tarihin al’ummar Gaba ba a taba kin baiwa al’ummar garin Sarkin da suka zaba ba, sai a wannan karon”

Ya ce duk lokacin da sarkin al’ummar ya rasu gidaje 13 ne za su taru domin zabar wanda zai gaje shi ko kuma su sanar da Babban sarkin yankin matakin da suka dauka.

“A wannan karon an samu ‘yan takara guda biyu, inda aka gudanar da zabe, Kuma Nan take ake sanar da sakamakon zaben, amma ba a taba Jan kafa wajan bayyana sakamakon zaben ba, har zuwa makonni uku. Ba a taba yin hakan ba,” inji shi.

Yayin da yake kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankulansu su guje wa tashin hankali, Mista Gana ya yi kira ga hukumomi da su kyale zabin mutanen da aka zaba, domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram