Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ce akwai matuƙar ƙonar rai yadda ran ɗan Adam ya zama ba a bakin komai ba a ƙasar.
Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook a ranar Lahadin nan inda ya ke jajanta ma waɗanda hare-haren ƴan ta’adda ya shafa a ƙananan hukumomin Giwa da Chikun da Zaria da Zangon Kataf na jahar Kaduna.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce dole ne a la’anci kashe mutane da ake yi siddan a cikin ƙasar.
“Ina addu’a da jajanta wa iyalan waɗanda hare-haren ƙananan hukumomin Giwa, Chikun, Zaria da Zangon Kataf na jahar Kaduna suka rutsa da su. Ina addu’ar samun jinƙan Ubangiji gare su”. In ji shi.