Mota Ta Taushe Ɓarawo Ya Mutu Yayin Da Ya Je Sata A Ƙarƙashinta

An ga gawar wani mutum da a ke zargin ɓarawo ne a ƙarƙashin wata mota a Ago Egun, bodar Idiroko da ke Jihar Ogun.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Jaridar Tribune ta rawaito cewa a na zargin ɓarawon ya yi yunƙurin kwance wasu muhimman abubuwa a jikin motar ne amma sai jak ɗin ɗaga mota da ya yi amfani da shi yayi
n ɗaga motar ya goce bayan ya riga ya shiga ƙarƙashin ta, inda motar ta faɗo masa.

Soji Gonzalo, Kwamandan rundunar bijilante ta jihar, ya baiyana cewa su na cikin sintiri ne sai su ka ga gawar mutum a ƙarƙashin wata tsohuwar mota a wani garejin gyaran mota.

Ya ƙara da cewa sun gano gawar mutumin ne da misalin ƙarfe 6 na yamma a Ago Egun ranar Alhamis.

Gonazlo ya baiyana cewa binciken su na farko ya nuna cewa motar ta daɗe a garejin wanda sama da shekara biyu ba amfani da ita kuma duk sun yi yunƙurin samun wanda ya ke da filin garejin a bin ya ci tura.

“A yanzu dai mun ɗauke gawar da kuma jak da mu ka samu mai launin ja da kuma almakashi da sauran sifanu za mu kai wa ofishin ƴan sanda na Idiroko domin faɗaɗa bincike,” in ji Gonzalo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram