Wasu Iyaye Sun Saida Jaririnsu Ɗan Wata Guda A Naira Dubu 50

Jami’an rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun sun kama wasu ma’aurata bisa zargin sayar da jaririnsu dan wata guda a kan kudi nera dubu 50.

Ma’auratan, Eze Onyebuchi da matarsa Oluchi Eze, kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana, suna zaune ne a Ilara da ke Ode Remo, a yankin karamar hukumar Remo ta Arewa da ke jihar ta Ogun.

Oyeyemi ya ce, wadanda ake zargin, an cafke su ne a ranar 16 ga watan Disamba 2021, biyo bayan labarin da ‘yan sandan Ode Remo suka samu cewa, ma’auratan wadanda ke zaune a titin Ayegbami, Ilara Remo, sun sayar da jaririn nasu ga wata mata da a halin yanzu ake nema ruwa a jallo domin kuwa ta rigaya ta arce.

Jaridar “Guardian” ta ruwaito cewa, jin labarin hakan ne ya sanya DPO na Ode Remo, CSP Olayemi Fagbohun, ya aike da jami’ansa na sirri zuwa yankin inda kuma suka samu nasarar damke matar da mijinta suka kai su ofishin ‘yan sandan.

A yayin da ake binciken wadanda ake zargin, sun gaya ma ‘yan sandan cewa, wata mata mai suna Ruth Obajimi ce ta hada su da matar da ta sayi jaririn nasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram