An Ƙone Ɓarayin Waya A Anambra

Wasu Fusatattun Mutane sun ƙone ɓarayin waya a Shate-talen Regina Caeli a cikin hutun ƙarshen mako akan hanyar Onitsha dake Awka, Babban birnin Jahar Anambra.

Acewar rahotanni, waɗanda ake zargin an kama sune a lokacin da suke ƙoƙarin sace wata waya a hannun masu wuce wa.

Amma wasu matasa sun kama su, inda suka kai su mahaɗar da aka ƙone su.

Onitsha, yankin Nkpor da Obosi a Jahar Anambra, wurare ne da suke ƙone ɓarayin waya, domin ya zamanto gargaɗi ga waɗanda suke tunanin yin sata.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Rundunar Ƴan sanda bata ce komai ba akan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram