An Ɓullo Da Wata Sabuwar Hukuma A Najeriya Da Za Ta Sa Ƴan Ƙasar Su Daina Mutuwa Da Wuri

Wata sabuwar hukuma da ake kira da Cibiyar Kula da Tsofaffi ta Najeria, NSCC, ta guduri aniyar ɓullo da shirye-shirye da za su tsawaita rayuwar al’ummar ƙasar wanda a turance a ke kira da ‘life expectancy’.

Jaridr Daily Nigerian Hausa ta ce, Darakta Janar ta cibiyar, Emem Omokaro ce ta baiyana hakan a wata ganawa da Kanfanin Daillancin Labarai, NAN a jiya Lahadi a Abuja.

Omokaro ta ci gaba da cewa, cibiyar za ta bunƙasa rayuwar tsufa har ta zama abar sha’awa a Nijeriya.

A cewar Omokaro a shekarar 2015 da 2018, Nijeriya tana ta can ƙasa a jerin ƙasashe masu tsayin rayuwa na duniya sabo da a lokacin babu wasu ajiyayyun bayanai da zai sanya ta kasance a saman jerin sunayen.

“A na yin jerin sunayen ne ta hanyar duba da irin kula da kuma jin daɗi da tsofaffi ke samu a ƙasa, da kuma wasu matakai da su ke yin nuni da hakan, misali, wa’adin tsawon rayuwa na tsofaffin mutane da dai sauran matakai.

“A Nijeriya, mutane su ke kaiwa shekaru 60, in ma sun kai, mutane nawa ne ke samun cikakkiyar lafiya da rayuwa bayan shekara 60 ɗin. Nawa ne a cikinsu su ke samun inshorar rayuwa da kuma kuɗaɗen kashewa?

“Amma yanzu, da zuwan NSCC,B wa’adin tsawon al’ummar Nijeriya zai ƙaru sabo da a yanzu muna da Doka ta Shekaru a Nijeriya. Mun tanadi wani kundin tsari na tsawon shekaru 10 sannan kuma dokar da ta kafa NSCC za ta taimaka gudanar da shirin,” in ji Omokaro.

Ta ci gaba da cewa” kwanan nan tsawon wa’adin shekarun ƴan Nijeriya zai ƙaru sabo da shirye-shiryen da mu ka tanada za su sanya ƴan Nijeriya su samu tsawon rai, za kuma a ƙarawa tsofaffi kulawa ta musamman,” in ji ta.

One thought on “An Ɓullo Da Wata Sabuwar Hukuma A Najeriya Da Za Ta Sa Ƴan Ƙasar Su Daina Mutuwa Da Wuri

  1. Idan gaskiyane gwamnati batason mutuwar jama,a anigeriya to meyasa take tilas taamana sai tayi mana allurar corona?.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram