Bankin AFDB Zai Taimaka Ma Najeriya Da Dala Milyan 210

Bankin raya kasashen Afirka ya amince da shirin ba Nijeriya bashin Dala miliyan 210 domin inganta ayyukan noman zamani a wasu jihohi da ake saran miliyoyin mutane zasu amfana.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin ya gabatar, tare da cewa bashin shine kashi na farko a shirin da za su hada kai da gwamnatin tarayya domin bunkasa ayyukan noma da samar da abinci.

Bankin ya kuma bayyana shirin a matsayin wanda zai bude kofar arzikin noman da Nijeriya ke da shi da kuma bunkasa masana’antu wajen samar da amfanin gonar da kiwo.

Sanarwar Bankin ya ce a karkashin shirin na farko jihohin Imo da Cross River da birnin Abuja za su amfana da tallafin kiwon dabbobi, domin samar da nama da kuma madara, yayin da jihar Kadauna zata amfana da shirin samar da tumatir da masara da kuma citta.

Jihar Kano kuma zata amfana da tallafin noman shinkafa da tumatir da gyada da ridi, jihar Kwara kuwa zata amfana da shirin kiwo, Ogun zata amfana da tallafin noman rogo da shinkafa da kuma kiwon kaji da kifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram