Shugaban hukumar shirya zaɓe ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar na buƙatar zunzurutun ƙuɗi har kimanin naira bilyan 305.
Farfesan ya bayyana Hukumar za ta buƙaci naira bilyan 305 domin gudanar da zaɓen shekarar 2023.
Shugaban ya ce kuɗin za su taimaka ma hukumar wajen yin shirinta a ciki shekara biyu sannan kuma za su samu damar yin duk wani zaɓen cike gurbi da ke da akwai a sassa daban-daban.
Shugaban ya kuma ƙara da cewa hukumar ta rigaya ta amshi bilyan 100 daga cikin bilyan 305 ɗin da ta ke buƙata.