Gwamnoni Sun Koyi Tabi’ar Buhari Ta Ƙin Zuwa Wuraren Da Ake Kashe-Kashe Jaje A Arewa – ACF

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa, (ACF) ta ce ayyukan Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da gwamnonin yankin arewacin ƙasar game da kashe-kashen ƴan fashi a hankalce na nuna cewa “rayuwarsu ce da ta iyalansu kaɗai ke da daraja”.

Ƙungiyar ta kuma ce gwamnonin na koyi da Buhari wajen ƙin ziyartar jama’ar da ƴan fashi suka addaba da hare-hare.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, ƙungiyar ta yi kira ga shugaba Buhari da gwamnonin da su “tausaya” wa mutanen da hare-haren ‘yan fashin daji suka shafa ta hanyar ziyartar wuraren.

“ACF na nuna rashin jin daɗinta game da abin da ya zama kamar wata liyafar kisa maras ƙarshe da ke faruwa a arewacin Najeriya,” kamar yadda sanarwar da sakataren ƙungiyar Emmanuel Yawe ya sanya wa hannu.

“Yayin da ACF ke bin sahun gwamnan Kaduna da shugaban ƙasa wajen yin alhinin waɗanda suka rasu, muna kuma kira ga dukkan gwamnatocin jiha da ta tarayya da su nuna ƙarin tausayi a irin wannan matsala ta rashin tsaro.

“Babu abin da zai hana shugaban ƙasa ko gwamnan jiha ziyartar irin waɗannan wurare. Mun lura cewa bai taɓa tunanin cewa ya kamata ya je ba. Hasali ma saboda koyi da suke yi shi, babu wani gwamna da ya yi hakan sai Babagana Zulum na Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram