Jiragen Yaƙin Habasha Sun Kashe Mayaƙan TPLF 28 A Yankin Tigray

Hare-haren da jiragen yaki da jirage marasa matuka sun kashe a kalla mutane 28 a yankin Tigray na kasar Habasha.

Hotunan da gidan Talabijin na Tigray TV ya nuna, wanda ‘yan tawayen TPLF ke iko da su ya nuna hotunan gawarwaki a kan tituna da wadanda suka jikkata ana kwashe su.

An kai harin ne wata kasuwa a garin Alamata dake yankin na Tigray..

Shugaban jami’an tsaro na garin Alamata, Ekubay Gebremedhin ya bayyana cewa: “Jirgin jirage masu saukar ungulu sun kai hari kasuwar inda su ka kashe mutane sama da 38 sannan sama da mutane 80 sun jikkata. Wadannan mutane ne da ke saye da sayarwa a kasuwar”.

Shugaban jami’an tsaron ya kara da cewa an fara kai hare-haren ne a ranar Larabar da ta gabata kuma sun shafe kwanaki uku a jere.

Gwamnati da kungiyoyin tawaye daban-daban sun shafe sama da shekara guda suna fafatawa a yankin na Tigray.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram