Rafael Nadal ya ce a ranar Litinin ya kamu da cutar Covid-19 lokacin da ya dawo Kasar Sifaniya daga Abu Dhabi inda ya halarci gasar ATP.
“Yanzu ina killace a gida kuma na sanar da mutanen da suka yi hulɗa da ni,” kamar yadda ya rubuta a shafin Twitter.
Idan za’a iya tunawa dai a karshen wannan watan ne dan kasar Sifaniyan ya tashi zuwa birnin Melbourne domin fafatawa a gasar ATP gabanin gasar Australian Open.