Babu Wani Zancen Gyara Ma Tubabbun Ƴan ta’adda Hali, Mu Aika Su Lahira Su Haɗu Da Allah Kawai – El-Rufa’i

Gwamna Nasiru El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun ‘yan ta’adda ba.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce bai yarda da shirin gwamnati na sauya wa yan ta’adda halaye ba tare da mayar da su cikin mutane Gwamnan ya ce babu wani tubabben dan ta’adda sai dai wanda ya mutu don haka ya ce shi abin da ya ke so shine a rika kashe yan ta’addan kawai El-Rufai ya bayyan hakan ne yayin zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a Abuja yayin da ya ziyarci Shuagba Buhari don masa bayani kan harin da yan ta’adda suka kai Kaduna

Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya ce, bai yarda da tsarin sauya wa ‘yan ta’adda hali ba, ya kara da cewa hanyar da ta fi dace wa a bi da su kawai shine su ‘tafi su gamu da Allah’.

Gwamnan ya bayyana matsayarsa kan batun ne a ranar Talata yayin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawa da Shugaba Muhamamdu Buhari, The Cable ta ruwaito.

El-Rufai ya ce tubabben dan ta’adda shine kawai wanda ya mutu.

Ya kai ziyara gidan gwamnatin ne domin yi wa Shugaba Buhari bayani kan harin baya-bayan da yan ta’adda suka kai inda suka kashe mutum 40 a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya yi wa gwamna El-Rufai rakiya zuwa gainin Buhari. Ya ce: “Babu wani abu mai suna tubabbun yan ta’adda. Dan ta’addan da ya tuba kawai shine wanda ya mutu. Niyyar mu shine mu kashe su (yan ta’addan), su tafi su ga Allah.”

El-Rufai ya ce an sun san inda yan ta’addan suke boye wa amma sojoji suna duba fararen hula da ka iya mutuwa ne idan an ce za a far musu a inda suke.

Akwai ‘yan ta’adda iri uku a Najeriya,

El-Rufai Gwamnan ya ce akwai yan ta’adda iri uku: Yan Boko Haram, Yan Bindiga da Yan Kungiyar IPOB kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce ayyana yan bindiga a matsayin yan ta’adda da aka yi a baya bayan nan ya bawa sojoji daman ragargazarsu da yakarsu.

El-Rufai ya bakuci shugaban kasa ya sake tura jami’an tsaro zuwa Kaduna domin samun daman magance matsalar.

Ya yi kira ga jami’an tsaro su kara zage damtse wurin ragargazan ‘yan ta’addan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram