Hisbah Ta Ce Za Ta Gayyaci Iyayen Wacce Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau Ta Najeriya

Hukumar Hisbah a jahar Kano ta ce za ta gayyaci iyayen…..wacce ta lashe gasar Sarauniyar ƙyau ta Najeriya don ta sanar da cewa wannan gasar haramun ne a addinin musulunci.

Shugaban hukumar Sheikh Munammad Ibn-sina ne ya bayyana haka a yayin wata fira da yayi da kafar sadarwa ta BBC.

Ibn-sina ya ce musulci bai bada dama ba ga mace musulma ta fito ta bayyana tsiraicinta da nusa wata gasa ko wace iri ce.

“Ita wannan Shatu Garko mun yi bincike an ce ƴar Garko ce musulma ce ma’ana ƴar asalin jahar Kano ce garinda Hisbah ta ke aikace-aikacenta.

Don haka za mu gayyaci iyayenta mu sanar da su illar yin ka don kada su zaci cewa yin wannan abin halal ne ta ci gaba da yi ko wasu su yi koyi da ita” In ji Shi Ibn-sina.

Ya ƙara da cewa shiga irin wannan ta kacici-kacici ko gasa ba ta halitta ba saboda tana koya ma ƴaƴa mata su fitar da tsiraicinsu da kuma rashin kunya.

Shugaban ya ce Allah ya faɗa a cikin Al’qurani mai girma cewa duk wata mumina muslama ta rufe jikinta ruf don kada ta fitar da tsiraicinta a cutar da ita.

Daga ƙarshe ya yi kira ga iyaye da su guji barin ƴaƴansu na shiga ko wace iri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram