Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa a shirye yake ya yi sasanci tare da kawo karshen duk wani bambanci da ke tsakaninsa da tsohon gwamna, Sanata Rabi’u Kwankawaso.
Gandujen ya ce, ya kamata a dakatar da wannan fada wanda ya jima ana yinsa.
Jaridar “Tribune” ta ruwaito cewa, Ganduje ya bayyana matsayin nasa ne a cikin wata hirar da ya yi da gidan rediyon Faransa.
Ganduje ya kara da cewa, kowa ya san zaman lafiya ya fi fada, ya kuma yi fatan Allah ya taimaki masu kokarin sasantasu da shiryasu duk da cewa akwai masu son rura wutar gabar don cimma burinsu.