Gwamnan jahar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Aminu Bello Masari, ya ce shi bai ga dalilin da zai sa a hana al’umma ɗaukar makamai domin kare kansu daga harin ƴan bindiga ba.
Masari ya bayyana hana ne a jiya Laraba a fadar gwamnati jim kaɗai bayan ya sanya ma dokar kasafin kuɗin shekarar 2022 hannu wanda majalisar dokokin jahar ta kai mashi
“Dole ne mu tashi tsaye mu kare kanmu, babu dalilin da zai sa mai kashe mutane ya riƙe makami sannan mutumin kirki ace ba zai riƙe makami ya kare kanshi ba” In ji Gwamna Masarin.
Gwamnan ya ƙara da cewa sun amshi jahar katsina cikin yanayi na satar dabbobi da kashe-kashe, ƙarshe sai abin ya koma satar mutane domin karɓar kuɗin fansa da ƙone-ƙone da lalata da matan mutane.
To cikin rahamar Allah yanzu mun samu sauƙin waɗannan abubuwa” ya ce.
Hakazalika ya ce idan aka yi la’akari da yawan jamin’an tsaron da ke akwai a jahar Katsina kuma a ce za a barsu su kaɗai da wannan faɗan to ya fi ƙarfinsu don haka dole ne sai mutane sun tashi tsaye domin bada gudunmuwarsu wajen yaƙar ƴan ta’addan.
Masari ya ce a jahar Katsina in aka ɗauke Funtua da Daura da Katsina sauran ƙananan hukumomin duk yawanci ƴan sandan da ke cikinsu ba su wuci su 60 ba ya ce kuma ga mutane da yawa.
“To saboda haka ashe kunga dole ne sai mun tashi mun taimaka mun bada gudunmuwa ta tsare kanmu da kanmu.