Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bar Villa Abuja, zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, inda daganan zai tafi Maiduguri, Babban birnin Jahar Borno.
A cewar Wakilin Majiyar mu, tawagar Buhari ta bar farfajiyar Aso Rock da misalin ƙarfe 10:04 na ranar Alhamis.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ziyarci domin ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamnatin Jahar ta ƙirƙira kuma ta kammala, a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum.
Jaridar The PUNCH ta bada rahoton cewa a ranar Talata Gwamna Zulum ya bayyana cewar Shugaba Buhari ya taimaki jahar sosai, kuma yayi sadaukarwa domin al’ummar jahar, su zauna cikin zaman lafiya, da lumana da cigaba.
Ya bayyana cewar Shugaba Buhari ya kashe sama da Dala Miliyan $50 domin samar da wutar lantarki ga Al’ummar Jahar Borno.
Haka zalika, a dai-dai lokacin da Shugaban Ƙasa ke kan hanya zuwa Maiduguri, Mataimakin Shugaban Ƙasar Yemi Osinbajo a halin yanzu, yana jagorantar taron Majalisar Zartaswa a daƙin taron Villa.