Ƴan bindiga Sun Harbe Ɗan Majalissar Dokokin Jihar Delta

Yan bindiga sun harbi Mamba mai wakiltar mazabar Ughelli ta kudu a majalisar dokokin jihar Delta, Hon Reuben Izeze, a daren jiya Alhamis, inda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka harbe shi a Effurun da ke karamar hukumar Uvwie a jihar Delta.

Duk da cewa bayanan harin sun kasance ba cikakku ba, harzuwa lokacin hada wannan labarin, Amma an gano cewa ‘yan bindigar sun bude wuta kan motar Izeze a kusa da wajen.

Vanguard ta ruwaito cewa dan majalisar ya tsira daga harin kuma a halin yanzu yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Majiyoyi sun ce daga bisani ‘yan bindigar sun sako direban dan majalisar da suka yi garkuwa da shi a yayin harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mista Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram