An Kama Wani Mutum Da Ya Ke Sayen Bindigogi A Wurin Tubabbun Ƴan ta’adda

An Gano Yanda Tubabbun Ƴan ta’adda Ke Ɓoye Bindigogi Daga Baya Su Sayar Da Su Ga Wasu Ƴan Bindigar.

Rundunar ƴan sandan jahar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta yi nasarar kama wani mutum da ya ke sayar da bin digogi ga ƴan ta’adda.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da Nasarar ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Katsina a ranar Alhamis.

Ɗan ta’addan mai suna Sani Mamuda wanda ake ma laƙabi da Shaɗari yana zaune ne a ƙauyen Shama da ke ƙaramar hukumar birnin Magaji a jahar Zamfara.

Jami’an ƴan sandan sun kama shi a kan hanyar ƙananan hukumomin Kurfi zuwa Batsari na jahar Ƙatsina, inda aka same shi da bindigigo ƙirar AK-47 ɓoye a cikin sit ɗin babur tare da harsashi guda 42.

SP Isah ya ce lokacin da suka binciki mai laifin ya shaida ma su cewa wasu tubabbun ƴan ta’adda, Mas’udu Ɗanbarno da Abdullahi Muɗalle waɗanda a kwanakin baya suka miƙa kansu ga jami’an tsaro da nufin sun tuba sun daina ta’addanci ne suka sayar mashi da bindigogin a kan kuɗi naira milyan 2 a cikin wani daji da ke yankin ƙaramar hukumar Mashi a jahar ta Katsina.

Mutumin ya ce zai kai bindigogin ne a jahar Zamfara wurin wasu ƴan fashin daji da suka bashi sautu suka kuma bashi la’adar dubu 80.

Ɗan ta’addar dai ya faɗi sunayen wasu mutane uku Sabe da Aliyu da Mande waɗanda su ma suke wannan harka ta saye da sayarwar bindigogi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram