Buhari Ya Ce Zai Ƙara Riƙe Alƙawuran Da Na Ɗaukar Ma Ƴan Najeriya Ba Zan Yi Sake Da Su Ba

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk alkawuran da ta yi ga ƴan ƙasar ba lokacin yaƙin neman zaɓe kafin cikar wa’adinsa.

Buhari ya bayyana haka ne a sakonsa na bukin Kirsimeti ga ƴan Najeriya, inda ya ce yana taya Kiristoci a Najeriya farin ciki kamar sauran mabiya a duniya don gudanar da bikin a wannan shekarar.

BBC ta ce, a cikin saƙon, shugaban ya roƙi ƴan Najeriya su yi rigakafin korona domin rage bazuwar annobar.

Ya kuma taɓo batun tsaro inda ya ce duk da nasarorin da jami’an tsaro suka samu amma har yanzu akwai ƙalubale.

“Ina kira ga ƴan Najeriya da su yi imani da mu da kuma ɗaukar abubuwan da ke faruwa a matsayin wani lokaci da kuma zai wuce, kamar sauran yanayi marar daɗi a tarihin ƙasar.”

“Wannan gwamnatin ba za ta yi watsi da alƙawullan da ta yi wa ƴan Najeriya ba,” in ji shugaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram