Da Ɗumi-ɗumi: Buhari Na Ganawa Da Shugaannin Hukumomin Tsaro Domin Lalibo Bakin Zaren

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Muazu Sambo a matsayin karamin ministan ayyuka da gidaje.

Sambo, wanda Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sa bayan tantance shi a farkon makon nan, ya yi rantsuwar ne kafin a fara wani taron tsaro da ake ci gaba da yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa kalubalen da ke tattare da rashin tsaro a fadin kasar nan a cikin sabbin barazana shi ne taron tsaro ya sa a gaba.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya halarci taron; Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (Mai Murabus).

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Manjo Janar Salihi Magashi Mai murabus; Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola; Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor; Babban Hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da kuma Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar, suma suna halartar taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram