Gasar Sarauniyar Kyau Ta 2021: Shawara Kawai Hisbah Za Ta Iya Bayarwa – Inji Wani Lauya

Wani lauya mazaunin Kano, Ali Jamilu, ya shawarci hukumar Hisbah ta Kano da ta rika lura da muhimman ayyukan da suka rataya a wuyanta, maimakon yin katsalandan a cikin batutuwan da ba su da wani mahimmanci.

Lauyan da ya ke magana kan batun Shatu Garko, wacce kwanan nan ta fito a matsayin Miss Nigeria 2021, ya ce abin da Hisbah ta fada dangane da bangarorin da suka duba, ta fuskar Musulunci, sun yi daidai.

“Hisbah an umurce su ne kawai su ba da shawara kan kyawawan dabi’un mutanen Kano kada su yi Allah-wadai ko ki ko tauye hakin kowa.”

“Ko da Miss Nigeria za a yi takara a Kano, Hisbah ba ta da hurumin hana ta. Babu wata doka da ta ba su wannan damar. Kuma babu wata doka da ta ba su damar hana duk wanda ke son tsayawa takara a Kano ko a wajen Kano. Kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa kowane dan kasa ‘yancin fadin albarkacin baki da tarayya har ya zuwa yanzu ba ta taka hakkin kowa ba kuma bata fita daga kan iyakokin doka ba.

“Yarinyar tana da ‘yancin yin cudanya ko bayyana ra’ayin ta a ko’ina. Tana da ‘yancin yin jituwa da kowa ko ƙungiya har ya zuwa yanzu wannan doka ne.

“Idan muka kalli mahanga ta addini, hakan yana tsakaninta da Allah da take bautamawa.

“Hisbah ba ta da wani hakki ko tushe na gayyatar iyayen Shatu da yi musu gargaɗi. Kuma ko da iyayen sun yanke shawarar ba za su amince da gayyatar ba sun yi daidai.

“Har ila yau, ya kamata kungiyar Hisbah ta yi taka-tsan-tsan ta hanyar rashin saba wa dokar da ta kafa hukumar ta ce. Aikinsu shine kawai nasiha bisa ga umarnin Musulunci.” Inji lauyan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram