Kungiyar Arsenal Na Zawarcin Coutinho

Kungiyar Arsenal ta kasar Ingila ta shiga sahun kungiyoyin kwallon kafar da ke yunkurin sayen dan wasan Barcelona, Philippe Coutinho a cikin watan Janairun 2022.

Dan wasan mai shekaru 29 da haihuwa, wanda ya bar Liverpool zuwa Barcelona a watan Janairun 2018 a kan zunzurutun kudi har Yuro miliyan 142, mai horas da kungiyar ta Barcelona a halin yanzu, Xavi Hernandez ya ce a kai kasuwa.

Baya ga Arsenal, kungiyoyin Everton da Newcastle su ma sun nuna sha’awarsu ta dauko dan wasan.

Ya zuwa yanzu dai a cikin kakar wasanni ta bana, Coutinho ya saka kwallaye 2 ne kacal a raga a cikin wasanni 16 da ya buga wa kungiyar ta Barcelona.

Kafar labaran wasanni ta “Sport” na da imanin cewa, duk da halin da Coutinho ke ciki, har yanzu zai iya yin daraja wajen sayarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram