Sojojin Najeriya Sun Kashe Kwamandan ISWAP Modu Kime A Borno

Rundunar sojin Najeriya ta kashe da Modu Kime, babban kwamandan kungiyar IS a yammacin Afirka (ISWAP).

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kashe Kime, wanda aka fi sani da Abou Maryam, bayan wani Arangama tsakanin Rundunar Soji da Mayakan ISWAP dake jibge a jihar Borno da kuma yankin tafkin Chadi.

An kai harin ne ta sama a gabar kogin Bisko da Tumbum Tawaye a karamar hukumar Abadam.

Tawagar leken asiri da sa ido da kuma binciken sirri (ISR) da rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) suka fallasa Maboyar mayakan

Wani jami’in tsaro ya shaida wa jaridar PRNigeria cewa Kime, wanda ya yi amfani da lambar waya +22788036182, ya kasance a kan komar ayyukan sashin leken asiri na kasar nan.

“Kime ya gudanar da aikin ne a kewayen Tumbum Tawaye, Bisko, Garere, Arkumma da Dumbawa, Zari da Gundumbali.

“Ya jagoranci kai hare-hare kan sojoji da wurare masu karancin tsaro galibi a kusa da Damasak, Nganzai, Gajiram da wajen Maiduguri,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram