Ƙungiyar Bayern Munich Ba Ta Buƙatar Haaland – In Ji Kahn

Shugaban Bayern Munich Oliver Kahn ya dage cewa babu bukatar komawa ga fitaccen dan wasan Norway Erling Haaland na Borussia Dortmund kamar yadda zakarun Bundesliga ta dauki Robert Lewandowski a baya.

Kahn ya bi layin da shugaban kulob din Herbert Hainer ya fada a baya lokacin da ya shaida wa Sueddeutsche Zeitung, cewa Lewandowski “zai ci gaba cin kwallaye 30-40 na tsawon shekaru biyu a nan gaba .”

Lewandowski na Poland ya kasance yana kafa tarihin zura kwallaye a cikin ‘yan shekarun nan, amma yana da shekaru 33 kuma yana da kwantiragin da Kungiyar zuwa 2023.

An ruwaito rahoton cewa Erling Haaland na da yarjejeniyar ficewa daga Borussia Dortmund, a bazara mai zuwa, wanda darajar kasuwar sa za ta yi kasa n.

Ana alakanta Real Madrid da zawarcin Haaland, wanda a zahiri yana da zabin manyan kungiyoyi a nahiyar idan ya yanke shawarar barin Borussia Dortmund.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram