Ƴan bindiga a Zamfara sun kashe mutane 10 tare da sace 35, bayan karɓar Naira Miliyan 15

Ƴan bindiga daɗi sun sace mutane 35, tare da kashe mutane 10 a ƙananan hukumomi 5 a Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jahar Zamfara.

Biyo bayan wannan lamari, ɗaruruwan mutane ne, suka bar gidajen su, a dalilin yawan kai hare-haren wanda ƴan ta’addan suke yi.

Mazauna karkarar sunce suna yi masu ta’addanci, duk da saka yarjejeniyar zama lafiya da akayi dasu ta za’a basu Naira Miliyan 15 domin su ƙyale su.

Ƙauyukan da suka biya jangalin sun haɗa da Karazau Dantsauni, da Gidan-Tsamiya, da Gurgurawa, sa Kwalaye, da kuma Gudan-kaura.

Majiyar mu ta ruwaito cewar, duk da biyan waɗannan maƙudan kuɗaɗen ga ƴan ta’addan, mutane 35 da suka haɗa da mata da ƙananan yara, wanda suka yanke shawarar tsayawa a garuruwan su, sun sace su, tare da kashe mutane 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram