AFCON 2022: Najeriya Ta Fitar Da Sunayen ‘Yan Wasan Da Za Su Buga Mata Gasar Cin Kofin Afirka

Mai horas da babbar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Augustine Eguavoen, ya sanar da sunayen ‘yan wasa 28 da za su buga wa kasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 33 wadda za a yi kasar Kamaru daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairun 2022.

Tsohon Kyaftin din Najeriyar, Eguavoen, wanda ya taba horas da kungiyar tare da kai kasar matsayi na uku a gasar a kasar Masar shekaru 15 da suka gabata, ya zabo masu tsaron gida 4 da ‘yan wasan baya 9 da yan tsakiya 5 da kuma ‘yan gaba 10 domin samun damar cin kofin a karo na 4, bayan da Najeriyar ta dauke shi har sau 3.

Daga cikin ‘yan wasan da aka gayyato akwai Kyaftin Ahmed Musa da Wilfred Ndidi, dan wasan tsakiya da Victor Osimhen, dan wasan gaba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar ‘yan jaridu da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta fitar a ranar Asabar.

Sauran ‘yan wasan da aka gayyaton sun hada da masu tsaron gida, Maduka Okoye da Francis Uzoho; ‘yan wasan baya, Kenneth Omeruo da Olaoluwa Aina da Abdullahi Shehu; ‘yan wasan tsakiya, Joseph Ayodele-Aribo da Chidera Ejuke da kuma ‘yan wasan gaba, Moses Simon da Odion Ighalo da Samuel Chukwueze.

Akwai kuma Kyaftin din kungiyar ‘yan kasa da shekaru 17, wato U-17 da suka ciyo wa kasar kofin duniya, Kelechi Nwakalli, da Emmanuel Dennis, da kuma wani tauraron gasar Olympics ta 2016, Sadiq Umar da kai sauransu.

Ana sa ran isowar dukkanin ‘yan wasan da aka gayyato Najeriya daga ranar 29 ga watan Disamba, 2021 zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2022, kamar dai yadda yake a cikin sanarwar.

Najeriya wadda ta ci kofin sau 3 za ta fafata ne da Masar, wadda ta dauki kofin har sau 7, da kasar Sudan da kuma Guinea Bissau a rukuninsu, kuma wasan farko a rukunin shine tsakanin Najeriya da Masar da za a yi a birnin Garoua a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram