Babbar Magana: Garba Shehu Da Lai Mohammed Da Wasu Na Kusa Da Shugaba Buhari Sun Kamu Da Cutar Korona

Sabuwar samfarin Cutar Covid-19 mai hatsari ta samu kutsawa a Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya da ake kira da Villa, a yayinda da yawa daga cikin masu taimakawa Buhari, da wasu manyan jiga-jigan Gwamnati, suka kamu da ƙwayar cutar.

Amma Gwamnatin ƙasar ta rufe maganar bata so a sani, a yayinda hatta wakilan Jaridu aka shawarce su, da kada su bada rahoto akan shigar cutar a Villa.

A binciken da jaridar PREMIUM TIMES tayi ya ce, Babban Sakataren a Fadar Shugaban Kasar Tijani Umar, da dogarin Buhari wato ADC Yusuf Dodo, da CSO nashi Aliyu Musa, da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa akan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu, wanda aka tabbatar da cewa suna ɗauke da cutar a cikin satin daya gabata, amma Ministan Yaɗa Labaru da Al’adu Lai Mohammed shima ya kamu da cutar.

Wasu daga cikin wanda cutar ta kama akwai Mr Garba, inda aka fita dashi daga taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba, a yayinda aka tabbatar yana ɗauke da cutar.

Garba Shehu wanda ya tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar a saƙon karta kwana, akan cutar a ranar Asabar, amma ya musanta cewa bashi da masaniya akan sauran waɗanda suka kamu.

Ya ƙara dacewa tuni ya samu sauƙi, inda yace bai daɗe da kammala motsa jiki ba, amma yana son yaga awo cewa ya warke daga cutar.

Saƙon shi yace “bani da masaniya akan sauran waɗanda suka kamu, amma ni na kamu da cutar Covid-19, naji na warke tun daga farko, domin ana Son mutum ya karɓi rigakafi guda uku, naji na warke garau, yanzu na kammala motsa jiki.

Dukkanin wani ƙoƙarin da akayi na ganin anji ta bakin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara akan Kafafen Yaɗa Femi Adesina akan lamarin bai samu ba domin wayar sa na nuna cewa ana kira wato-“busy” a lokacin da aka kira shi, haka zalika bai maido da saƙon da aka tura mashi ba, bayan awanni da aika masa shi.

A ɓangaren shi, Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa akan Kafafen Sadarwa na zamani Tolu Ogunlesi, yace bazaiyi magana ba akan lamarin, inda ya bayyana ƴan jarida a matsayin masu magana da bakin Gwamnati.

Duk ƙoƙarin ganin anji ta bakin Ministan Yaɗa Labaru Lai Mohammed bai samu ba, domin wayar shi a kashe take na tsawon awanni 24, inda mai taimaka masa Segun Adeyemi bai ɗauki waya ba, bai kuma maido da saƙon da aka aika mashi.

Majiya mai tushe tace Mr Mohammed da sauran manyan jiga-jigan Gwamnati sun killace kansu, suna karɓar magani.

Haka zalika wata majiya tace kulle ofishin Matar Shugaban Ƙasa Aisha Buhari, to matakin baya rasa nasa ba, da manyan jiga-jigan Gwamnati a fadar shugaban ƙasa da suka kamu da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram