Bukukuwan Kirismeti: Mutane 7 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Shagamu, Hanyar Benin

Mutane 7 ne suka mutu, yayin da wasu bakwai suka samu raunuka a ranar Asabar a wani hatsarin da wata motar alfarma kirar Mercedes Benz ta yi a gadar Ososa da ke kan hanyar Sagamu zuwa Benin.

Ahmed Umar, babban kwamandan hukumar FRSC a Ogun ya tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta.

Malam Umar ya ce hatsarin ya afku ne da karfe 12:20 na safe kuma ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri da direban ya yi.

Ya ce motar da ba ta yi rajista ba ta taso ne daga Ojuelegba da ke Legas, kuma ta nufi yankin gabashin kasar ne a lokacin da hatsarin ya afku.

Ya kara da cewa mutane 63 – da suka hadar da maza 40, manya mata 15 da yara takwas suna cikin motar bas din kuma 49 daga cikinsu ciki har da yaran sun tsira ba tare da jikkata ba.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata an Kai musu agajin gaggawa yayin da aka kwantar da wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Asibitin jihar da ke Ijebu-Ode a jihar Ogun.

Kwamandan sashin ya gargadi masu ababen hawa game da tukin gaggamci, musamman a wannan lokacin da ake yawan zirga-zirgar ababen hawa da tafiye-tafiyen dare a lokacin bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara.

Ya shawarci masu ababen hawa da su rika kiyaye gudun wuce kima, da guje wa tafiye-tafiye da daddare da kuma bin ka’idojin tuki.

Umar ya jajanta wa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, ya kuma umurce su da su tuntubi sashin Hukumar FRSC Ijebu-Ode domin jin karin bayani game da hadarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram