Babban Hafsan Sojin Ƙasa Laftanar-Janar Faruƙ Yahaya ya bada umarnin ayi gaggawar saki Sojar da ake tsare da’ita, Hannah Sofiat.
Sofiat dai ta karɓi tayin auren ta, ga wani Mai bautar Ƙasa a sansanin horas da matasa masu yiwa ƙasa hidima dake Yikpata, Kwara.
Haka zalika, wata majiya daga soji ta sanar da cewa a ranar Asabar ne, Babban Hafsan Sojin Najeriya ya shiga lamarin, inda ya bada umarnin a yafe mata.
Majiyar tace Hedikwatar rundunar Sojin Ƙasa ta ɗauki wannan matakin ne domin nuna murna da bukukuwan Kirsimeti.
Majiyar tace an gargaɗi sojar, sakamakon karya dokar gudanar da aikin soji, yana mai cewa an yafe mata, tare da bada umarnin taje wajen ƴan uwanta da abokanai domin bikin murnar Kirsimeti.
A cewar majiyar, wannan mataki an ɗauke shi ne domin tabbatar da ingantattun soji dake da manufar samar da tsaro a Najeriya.
Sofiat dai an tsare ta sakamakon karya dokar sojin ƙasa da tayi, ta hanyar nuna dangantakar ta da farar hula a wajen bada horo.
An dai tsare ta ne bayan wani bidiyo da yayi yawo, inda aka ganta tana karɓar tayin auren ta, daga wani matashi mai yiwa ƙasa hidima a sansanin horas da su dake Kwara.
Mutane da dama sun ta yin kira ga Rundunar sojin da suka saki Sojar.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun Rundunar Sojin Ƙasa Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da lamarin.