Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce a yanzu galibin dazuzzukan ƙasar sun zamma maboyar ƴan ta’adda, da ƴan fashi da makami da ƴan bindiga da masu aikata laifuka.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawar sirri da ya yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja kan matsalar tsaro a jiharsa.
Ya bayyana kalubalen tsaro da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu da cewa abin takaici ne, ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa da ya taimakawa gwamnonin jihohi.
Gwamnan ya buƴaci a kafa wani sansanin horas da sojoji a dajin da ke kan iyaka da jihohin Kano, Kaduna, Bauchi da Filato, domin duba ayyukan ƴan ta’adda.
“Akwai ƙalubale a duk fadin kasar nan waɗanda abin takaici ne, amma mun yi imanin cewa shugaban ƙasa yana yin iya ƙoƙarinsa tare da sauran masu ruwa da tsaki domin daƴile lamarin.
“Muna bukatar taimakon kusan kowa da kowa, musamman gwamnoni da shugabannin ƴananan hukumomi. Mun lura cewa matsalar tsaro a yanzu, dajin mu ne manyan matsalolin saboda suna daukar ƴan bindiga, ƴan ta’adda, da ƴan fashi da makami kuma suna karɓar waɗanda suke da laifuka daban daban.
“A jihar Kano mun ɗauki wasu matakai. Muna da manyan dazuzzuka guda biyu, dajin Falgore, wanda ke kan iyaka da Kano, Kaduna da Bauchi, shi ma ba shi da nisa da Filato. A wannan dajin, mun kafa sansanin horar da sojoji tare da hadin gwiwar Sojoji,” inji shi.