Ƴan Bindiga Sun Sace Surukin Rochas, Yana Tsaka Da Ibada A Wata Coci Dake Imo

Akwai rudani da fargaba kan wani lamari da ya shafi Uche Nwosu, surukin Sanata Rochas, tsohon gwamnan jihar Imo.

Nwosu, wanda ya tsaya takarar gwamna a zaben shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar Action Alliance wato AC, an Yi awan gaba da shi a cocin St Peters Anglican, dake yankin Eziama Obire a karamar hukumar Nkwere na jihar Imo, yau Lahadi.

Babu tabbas ko ‘yan bindigar jami’an tsaro ne ko kuma masu garkuwa da mutane ne, yayin da su kai ta harbe-harbe ta iska a lokacin da suka afka Cocin don tafiya da shi.

Nwosu yana halartar taron godiyar da Addu’a na mahaifiyarsa da aka binne kwanan nan, lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari.

A cikin wani faifan bidiyo, an ga wanda abin ya shafa a na tilastama shi shiga wata mota, yayin da masu kallo ke kururuwa daga nesa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram