Rahotanni sun bayyana cewa Arsenal na fatan kulla yarjejeniya da Bukayo Saka na tsawon shekaru shida har zuwa lokacin bazara na shekarar 2027.
Arsenal za ta yi hakan ne, Dan wasan na Ingila ya ci gaba da samun nasara a karkashin kocin Mikel Arteta inda kuma ya yi nasarar zura kwallaye hudu kuma ya taimaka a ciki hudu a wasanni 20 da ya fafatawa kungiyar duk gasa a bana.
A bara ne Saka ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar, inda a halin yanzu wa’adinsa ya zai Kai har zuwa karshen kakar wasa ta 2023/24.
Sai dai dan jarida Ekrem Konur ya yi ikirarin cewa a yanzu Arsenal ta kuduri aniyar rike dan wasan mai shekaru 20 na tsawon lokaci, tare da kulla yarjejeniya har zuwa shekarar 2027.
Irin wannan kwangilar za ta ci gaba da sa Saka ya zauna a kulob din bayan cika shekaru 25.
Ba a san halin da ake ciki game da sauran Yan wasan gaban na Arsenal ba, kodayake, Arteta ya yarda cewa akwai “rashin tabbas” kan makomar wasu ‘yan wasansa.