Duk Macen Da Za Ta Yi Tafiya Kar A Barta Ta Tafi Sai Da Makusancinta Namiji – Taliban

Gwamnatin Taliban a Ƙasar Afghanistan a ranar Lahadi, tace dukkanin matan dake son yin ziyara ko tafiya, indai bata kusa bace, to kada a barsu su tafi, har sai sun tafi da makusancin su Namiji.

Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Ma’aikatar Hana ayyukan ashsha ta fitar, inda tayi kira ga masu ababen hawa, dasu ɗauki mata kaɗai waɗanda ke sanye da Hijabin Musulunci.

“Matan da zasu yi tafiya data wuce kilomita 72, to kada a ɗauke su har sai sun tafi da makusanci,” inji Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Sadeq Akif Muhajir suka gayawa Kamfanin Dillancin Labaru na AFP a ranar Lahadi, suna masu cewa dole makusantan su zama Namiji.

Wannan takarda dai an fitar da’ita, makonni kaɗan bayan Ma’aikatar ta buƙaci gidajen talabijin na Ƙasar dasu daina nuna duk wani wasan kwaikwayo da aka sanya mata a ciki.

Ma’aikatar ta kuma buƙaci ƴan jarida mata da su riƙa sanya Hijabi idan suna gudanar da harkokin su na aikin su.

Muhajir a ranar Lahadi yace, za’a buƙaci Hijabi ga dukkanin matan dake neman yin tafiya. Ma’aikata ta kuma umarci mutane dasu daina sanya kiɗa a ababen hawa nasu.

Tun watan Ogusta da Taliban da ƙwace iko da Gwamnatin Afghanistan, ta sanya dokoki da dama akan mata, duk da sun sha alwashin yin mulki mai sauƙi, idan aka kwatanta da wanda suka yi a shekarar alif 1990.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram