Mu Turji Zai Faɗa Ma Sulhu, Shi A Wa? – In Ji Gwamna Masari

Gwamnan kajar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Aminu Bello Masari ya mayar da raddi ga fitaccen ɗan ta’addar nan, Bello Turji bisa ga wasiƙar da ya rubuto cewa yana buƙatar a yi sulhu da shi.

Masari ya mayar masa da martanin ne a cikin wata murya da wakilin DW a Katsina ya tattauna da shi game da sha’anin tsaro da wani ɓangare na zaɓen ƙanana hukumomi.

“Ai sulhu da wa, mu a gaya mana sulhu, ƙarya ya ke, kuma ai sulhu shi a wa, akan me, ka je waɗanda ya kashe ya ƙona masu gari ya ƙona iyayensu ya kashe ƴaƴansu ka gaya masu wannan maganar. Har wani ƙa’ida, ƙa’ida ta me?” In ji Gwamnan.

A kwanakin baya dai ne Bello Turji ya rubuta wasiƙar wacce a cikinta ya ke neman jami’an tsaro da su tsaigai da wutar da suke buɗe masu a cikin daji domin ai sulhu kuma a cikin takardar ya shimfiɗa wasu ƙa’idoji da gwamnati zata bi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram