Nan Da Watanni 3 Masu Zuwa Za Ai Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Katsina – In Ji Masari

Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana gudurinsa na yin zaɓen ƙananan hukumin jahar a cikin sabuwar shekarar 2022.

Masari ya bayyana haka ne a yayin wata fira da wakilin DW a Katsina ya yi da shi.

Gwamnan ya ce nan da watanni uku masu zuwa gwamnatinsa za ta yi zaɓen a dukan ƙananan hukumomin 34 da ke faɗin jahar.

Masari ya ce dama dalilin da yasa ba a yi zaɓen ba sabo maganar da ta ke gaban kutu to kuma shari’ar ta ƙare inda kotun ƙoli ta koreta tare da umartar gwamnatin jahar da ta biya shugabannin ƙananan hukumomin da ta soke wanɗanda suka ci zaɓe a ƙarkashin jam’iyyar PDP kafin daga bisa gwamnatin APC da ta zo ta rushe su.

Sai dai kuma Masari ya ja kun ne da cewa yana so a san da cewa ko an yi zaɓen ƙananan hukumomi 18 ne kaai daga cikin 34 za su iya biyan albashin ma’aikata sauran 16 duka sai an taimaka ma su.

Ya ce don haka mutane kar su sa ran cewa in an yi zaɓen ƙananan hukumomin wasu kuɗaɗe ne za a kai ma su domin ai shagali.

Daga ƙarshe gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta zaɓi mutanen da za su ja gaba wajen amso haƙƙin ƙananan hukumomi a kasuwanninsu domin su yi amfani da su wajen kawo ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram