Wani da ake zargin Matsafi ne mai suna Alfa Tunde Olayiwola Wanda yake tsare a ofishin ƴan sanda akan zargin sa ɗauke da kan mutane ya faɗi, ya mutu a ranar Asabar.
Ƴan sandan sun bayyana haka a ranar Lahadi.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Ondo DSP Olufunmilayo Odunlami Wanda ya tabbatar da mutuwar wanda ake zargin, ya ƙaryata cewa zargin cewa sun lakaɗa masa duka har ya mutu.
Odunlami yace wanda ake zargin yana yin wasu ɗabi’u wanda ba’a gane mashi ba a ranar Asabar da yamma, inda akayi saurin kaishi Asibiti, amma daga bisani aka tabbatar ya mutu.
“Ko a Asibitin bai nuna wata alama ba ta cutar dashi, domin ba’a cutar dashi ba.
“Waɗanda suke shaida a lokacin da aka gabatar da Olayiwola ga ƴan jarida, sun ga cewa ba’a cutar dashi ba,” inji Odunlami.
Kwamishinan Ƴan sanda a Jahar Ondo Mr Oyeyemi Oyediran ya gabatar da Olayiwola a gaban manema labaru a ranar 23 ga watan Disamba a Akure tare da wasu da aka kama da zargin aikata ta’addanci.