Wasu Ƙauraye mafarauta a ƙauyen Udawa na ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna sun kama wani ɗan bindiga a wani daji da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Jaruman mafarautan sun kuma kuɓutar da wasu mutanen ƙauyen su 9 da aka yi garkuwa da su a farmakin da suka kai wa ƴan bindigar da ke addabar yankin.
BBC ta ce, Jaridar Aminiya ta rawaito cewa mafarautan sun yi wa ɓarayin kwanton ɓauna ne kwanaki bayan da suka far wa ayarin motocin matafiya a kan babbar hanyar.
Wani mai faɗa a ji a yankin Muhammad Umaru ya ce dukkan wadanda aka ceto daga ƙauyen Udawa ne.