Ƙarya ake yi man, bana ɗauke da cutar Covid-19, inji Lai Mohammed

Ministan Yaɗa Labaru da Al’adu Lai Mohammed ya ƙaryata rahoton dake cewa yana ɗauke da cutar Covid-19.

Ana tsaka da rahoton cewa wasu masu taimakawa Shugaban Ƙasa sun kamu da Cutar, Ministan yace shi bai killace kansa ba, kuma baya Asibiti domin karɓar magani.

“Ministan baya ɗauke da cutar, don haka baya a killace ko kuma karɓar magani a ko’ina, ” inji Mai Taimaka masa akan kafafen yaɗa labaru Segun Adeyemi, a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi.

“Rahoton wanda wata Jarida a kafar sadarwa ta zamani ta fara bugawa, inda wasu suka ɗauke shi daga nan, ya nuna irin matsalolin da muke fuskanta wajen gangamin mu na yaƙi da Labarun Ƙarya.

“Karatun Jarida ya nuna cewa idan kana kokwanto kabar abun kawai’ kuma yana cikin ƙa’idojin aikin Jarida na faɗin gaskiya, sahihanci da sauran su. Rahoton bai ƙunshi waɗannan abubuwa ba.’

A cewar Adeyemi, Lai Mohammed ya halarci taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa a ranar Laraba, da wani taron a ranar Alhamis, gami da rantsar da sabon Ƙaramin Ministan Ayyuka da gidaje a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewar ogan shi ya yi taron Manema Labaru akan taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa, to taya ya zaiyi wadannan ayyukan yana a killace.

Mai magana da yawun Ministan yace a matsayinsa na mamba a Kwamitin Fadar Shugaban Ƙasa akan cutar Covid-19, Lai Mohammed bazai ji ƙyashin sanar da al’umma cewa yana ɗauke da cutar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram