An Son Ƴaƴan PDP Su Haɗa Ƙai Don Lashe Zaɓen 2023

Ku haɗa kan ɓangarorin dake rikici da Juna a PDP– Wata Kungiya Ta Bukaci NWC

An bukaci kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa da ya hada kan bangarorin da ke rikici da juna a jam’iyyar tare da shirya su, domin samun nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban kungiyar PDP Unity Forum da ke Zaria a jihar Kaduna, Barr Yusuf Sambo ne ya yi wannan roko yayin da yake zantawa da Jaridar Daily Trust a jiya.

Ya ce jam’iyyar ta shiga rudani da yawan shari’o’in kotu da kuma gungun bangarorin da ke barazana ga damarta na cin zabe a nan gaba.

“Wannan ne lokacin da ya dace da za a fara tsara jam’iyar, kuma a fara tsara yadda za a hada kan bangarorin da ke gaba da juna don samun nasarar jam’iyyar baki daya,” in ji shi.

Sambo ya kalubalanci masu ruwa da tsaki da su fara bullo da dabarun siyasa wajen dinke baraka a tsakanin magoya bayan jam’iyyar ta PDP domin gujewa sauya sheka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram