Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Sokoto, Alhaji Bello Goronyo, ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da rike madafun ikon jihar a shekarar 2023.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta kammala shirye-shiryen karbar wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar.
A wata hira da manema labarai a jiya, Goronyo ya ce irin ayyukan da gwamnatin PDP ke jagoranta a jihar zai ba ta damar lashe zabe mai zuwa.
‘Yan adawa suna kishin ayyukanmu. Ba sa jin daɗin nasarorin da muka samu domin ba sa tsammanin za mu yi yadda muke yin.” Inji shi.
Ya kara da cewa “Suna cikin tashin hankali saboda sun san a matakin da muke tafiya, 2023 za ta kasance mai nasara a garemu, da yardar Allah,” in ji shi.
“Muna shirin karbar da dama daga cikinsu (’yan APC) daga Bodinga da sauran sassan jihar. Muna so mu mai da shi bikin kaddamar da Tubalin Nasarar mu, shi ya sa aka samu jinkirin karbar su,” inji shi.
Ya yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa shugabannin PDP na shiga lungu da Sako domin janyo hankali ‘yan adawa da shiga jam’iyar.