Rundunar Ƴan sandan Jigawa Ta Kama Ɓarayin Shanu

Rundunar Ƴan sandan Jahar Jigawa ta kama wasu mutane guda biyu da laifin satar shanu a Ƙaramar Hukumar Garki ta Jahar.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan sanda Jahar ASP Lawan Shiisu ya bayyana haka a Dutse a ranar Litinin.

Shiisu ya bayyana cewar, bayan sun ji labarin satar shanun, suka tura jami’ai domin ganowa, inda suka gano su a kasuwar Wudil ta Jahar Kano.

Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar ya ƙara dacewa waɗanda ake zargin sun ƙunshi ɗan shekaru 30 mazaunin Jaya dake Garki, da ɗan garin Daware dake ƙaramar hukumar Ringim, duk an kama su da tsunduma domin aikata laifin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram