Al’haki: Ɓarawo Ya Kare Ƙafa A Yayin a Ya Saci Motar Assibiti Ta Ɗaukar Marasa Lafiya

Rundunar ƴan sandan jahar Kano da ke Arewacin Najeriya ta kama wani ɓarawon motoci mai suna Saminu Sanusi mai shekaru 40 da ya saci motar assibiti ta ɗaukar marasa lafiya.

Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a cikin wani hoton bodiyo da ya sanya a shafinsa na facebook.

Ya ce an samu nasarar kama ɓarawon ne a daidai lokacin da ya ke yunƙurin ficewa da motar daga Najeriya zuwa Ƙasar Nijar, a daidai kan bodar Ɓaɓura a cikin jahar Jigawa.

Ya ƙara da cewa an kama ɓarawon ne tare da taimakon al’umma.

Kiyawa ya ce a lokacin da suka kama ɓarawon yayi ƙoƙarin guduwa inda a yunƙurin guduwar ne ƙafarsa ta kare.

Ɓarawon motar wanda ƴan sandan suka ce sun kama shi kusan karo na uku kenan da irin wannan laifin, ya amsa aifinsa laifinsa.

Kakakin rundunar ya ce da zaran an kammala bincike za su tura shi zuwa kotu domin ya fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram