Har Yanzu Ina Kan Ra’ayina Na Cewa A Maida Shugabancin Najeriya Hannun Ƴan Kudu – Masari

Gwamnan jahar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ya sake jaddda ra’ayinsa na cewa ya kamata a maida shugabancin ƙasar hannun mutanen Kudu.

Masari ya sake bayyana ra’ayin nasa ne a ranar Talatar nan a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin jahar.

Masari ya ce ko da kundun tsarin mulki bai ce a yi tsarin karɓa-karɓa ba amma kuma ba laifi ba ne in aka yi hakan.

Gwamanan ya ce ƙasar nan na buƙatar ta ci gaba da kasancewa a matsayin ƙasa guda don haka maida mulkin a hannun mutanen kudu zai taimaka gaya wajen ƙara zamanta na dunƙulallar ƙasa.

A kwanakin baya ne dai gwamnan ya yi wannan magana wadda da dama takwarorinsa na sauran jahohi ba su yi na’am da batun ba.

“Ko babu wani gwamna da ya yarda da wannan ra’ayin nawa, ni a matsayina na Aminu Masari wannan ra’ayina ne a matsayina na ɗan ƙasa”. In ji Gwamnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram