In Har Ka Cika Kai Namiji Ne Ka Fito Lokacin Da Ƴan ta”adda Suka Kawo Hari A Garuruwaku – Masari

Gwamnan jahar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya, Aminu Masari, ya ƙalubalanci masu shiraya zanga-zanga a tare hanya ana hana motoci da matafiya wucewa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin ganawa da manema labarai a ranar Talatar nan a fadar Gwamnatin jahar.

Ya ce bai kamata ba ƴan ta’adda sun kawo hari a ƙauyenku amma ku shige cikin bukka ku ɓoye sai sun gama ta’asarsu sai ku fito ku kama zagin mai unguwa da sauran shugabanni.

Gwamnan ya ce bai dace ba masu zanga-zanga su riƙa tare hanyoyi sabada suna cuta ma sauran bayin Allah musamman marasa lafiya da ƴan kasuwa da matafiya wanda yin hakan cutarwa ne matuƙa.

“In har ka cika namiji ne kai ka fito lokacin da ƴan ta”adda suka kawo hari a garuruwaku ba sai sun gama ta’asarsu ba ka fito ka kama zagin mai unguwa ko DPO da sauran ahugabanni”. In ji Gwamnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram