Ka Guji Ɓata Ma Gwamna Hope Uzodinma Suna – Gargaɗin APC Ga Rochas Okorocha

Jam’iyyar APC reshen jihar Imo, ta shawarci Sanata Rochas Okorocha da ya daina bata sunan Gwamna Hope Uzodinma da ikirarin karya da kuma hawayen karya, da nufin yana tausaya wa ‘yan Najeriya.

Jam’iyya mai mulki karkashin jagorancin Macdonald Ebere ta ce, “A matsayinmu na jam’iyya, muna ba Rochas Okorocha shawara da ya guji yin zagon-kasa da kokarin da yake yi na alakanta Sanata Hope Uzodimma da halin da ya ke ciki”

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar, Cajetan Duke, a ranar Litinin.

APC ta ce kasancewar Uche Nwosu wato Sirikin Rochas bai ba shi kariya daga kamawa da gurfanar da shi a gaban kotu ba, saboda auren diyar tsohon gwamna ba shi da kowace irin kariya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A matsayinmu na jam’iyya, muna ba Rochas Okorocha shawara da ya guji yin zagon kasa da kuma kokarin da yake yi na alakanta Sanata Hope Uzodimma da halin da yake ciki na son rai.

“Jam’iyyar APC tana sane da cewa doka ba ta kyale kowa ba, saboda babu wanda ya fi karfin ta.

“Hakazalika, doka za ta sa a kama mutum da karfi muddun yaki amsa kayyatar jami’an tsaro, don gurfanar da mutumin.”

Jam’iyyar APC ta yabawa Uzodimma bisa halin da ya nuna wajen fuskantar tashe-tashen hankula da nuna wariyar launin fata daga mutanen da suka yi gangancin aikata laifin cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram